Taron Gaggawa Na ECOWAS Da Matakan Da Ta Dauka

Your browser doesn’t support HTML5

A wani taron gaggawa da ta yi a Abuja a kan juyin mulkin a Nijar, kungiyar ECOWAS ta bai wa sojojin kasar wa’adin mako guda da su mayar da gwamnatin Mohamed Bazoum ko kuma ta dauki dukkan matakin da ya dace – wanda ya hada da yiwuwar amfani da karfin soji.