Sabani kan manyan akidu ya dagula burin Sweden na samun shiga kungiyar kawancen tsaro ta NATO, fadadawar da ke bukatar gaggawa bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, amma tana bukatar amincewar daukakin manbobin kungiyar na yanzu.
Tun a bara Turkiyya ta dakile damar shigar Sweden cikin kungiyar, bisa dalilan da ta zayyana da suka hada da boren kin jinin Turkiyya da na kin jinin musulunci a Stockholm.
Sai ga shi a makon jiya wani kirista dan gudun hijirar kasar Iraqi ya kona Alkur’ani a wajen wani masallaci a Stockholm a yayin gudanar da sallar idin babbar sallah, aika-aikar da mutumin ya ce, tana bayyana yadda ya ke ji ne game da Alkur’ani.
Kona Alkur’anin ya janyo Allah wadai daga kasashen musulmi, da kuma bore dabam-dabam daga masu tsatstsauran ra’ayi, ya janyo mahawara a kasar ta Sweden game da iyakar fadin al’barkacin baki. A yanzu yan sandan Sweden sun ce sun karbi sabbin bukatun iznin gudanar da zanga-zanga daga daidaikun jama’a da ke son kona Al’kurani har ma da litattafan Attaura da Linjila.
Kasashen musulmi sun bukaci Sweden da ta sa doka, yayin da shugaban Pakistan Shehbaz Sharif ya yi kiran a yi zanga-zangar tabbatar da kare mutuncin littafi mai girma na musulmai a lokacin sallar Juma’a, yayin da majalisar dokokin Pakistan din za ta tattauna batun kone Al-qur’anin.
~Hauwa Sheriff