Shugaba Tinubu Zai Hallarci Taron Kolin Tattalin Arziki a Paris

Dawowar Zababban Shugaban Najeriya Ahmed Bola Tinubu Najeriya Bayan Kammala Hutu A Ketare 2

Sabon shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu zai yi balaguro zuwa kasar waje a karon farko tun bayan ya karbi ragamar mulki a ranar 29 ga watan Yunin shekarar ta 2023

A ranar Alhamis , 22 ga watan Yunin 2023 ne ake sa ran shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai tashi zuwa Paris, babban birnin kasar Faransa, inda zai gana da sauran takwarorinsa na kasashen duniya wadanda ake sa ran za su tattauna kuma su rattaba hannu akan wata sabuwar yarjejeiyar tattalin arzikin duniya wato ‘Global Financial Pact.”

Yarjejeniyar za ta baiwa kasashe masu raunin tattalin arziki fifikon kasancewa kan gaba wajen samun tallafi da kuma zuba jari.

Kasashen da ke cikin wannan rukuni su ne kasashen da suke kan gaba wajen fuskantar matsalolin sauyin yanayi da na makamashi, kana sun kasance kasashen da suka fi jin radadin annobar COVID-19.

Wata sanarwar da daga ofishin mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan ayuka na musamman Dele Adeleke, ta bayyana cewa shugaban zai halarci taron kolin na wuni biyu daga ranar Alkhamis zuwa Jumma’a, 23 ga watan Yunin 2023.

Ana sa ran taron zai atattuna kan yiwuwar sake duba kasashen da suke fuskantar kalubalen tattalin arziki a gajeren zango , musamman ma wadanda bashi yayi musu katutu domin samo musu dabarun zamani na tattalin arziki wanda zai taimaka musu waje tunkarar hadarin matsalolin sauyin yanayi.

Dawowar Zababban Shugaban Najeriya Ahmed Bola Tinubu Najeriya Bayan Kammala Hutu A Ketare 1

Kazalika, taron zai mai da hanakali wajen inganta ci gaban kasashen da suke samun karancin kudaden shiga, kana ya karfafa zuba jari a fannin makamashi mai tsafta musamman domin yunkurin da duniya take yi na sauya amfani da makamashi mai tsafta domin kasashe masu tasowa.

Sanarawar ta kuma bayyana cewa, shugaba Tinubu da sauran shugabannin kasashen duniya, manyan kamfanoni, masana harkar kudi da kwararru a sha'anin tattalin arziki za su yi duba na tsanaki akan farfado da komadar tattalin arzikin kasashe daga radadin annobar COVID-19 da karuwar matsalar talauci, tare da zummar samar da damar samun kudade da kofar zuba jari wanda zai haifar da ci gaba mai dorewa.

Lokacin da Tinubu ya sauka a Abuja (Hoto: Facebook/Kashim Shettima)

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ne zai kasance mai masaukin baki a taron wanda za'a gudanar a Palais Brongniart.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Tinubu zai sami rakiyar mambobin majalisar shugaban kasa masu ba da shawara akan dokokin kasa da kuma manyan jami'an gwamnati.

Ana sa ran Tinubu ya dawo gida Najeriya a ranar Asabar, 24 ga watan Yuni bayan kammala taron.