Mutanen da suka rasa matsugunansu a sansanin ‘yan gudun hijira na Minawao da ke kan iyakar Kamaru da Najeriya, sun ce adadin mutanen da ke neman agajin jinkai a sansanin na karuwa a kowace rana.
A lokacin da ya yi magana da Muryar Amurka, Isaac Luka, shugaban ‘yan gudun hijira na Najeriya a Minawao, ya ce kwararowar ‘yan gudun hijira da ake gani yanzu saboda yunwa da tashin hankalin bindiga na kara tsanta yanayin rayuwa a sansanin.
“Akwai ‘yan Najeriya da suka fito daga garuruwan da ke kusa da iyakar. Ana ba su filiye don su fara noman abinci, amma yanayin damina ya shafi amfanin gona a kakar bana, kuma yawan kai hare-haren ‘yan bindiga a yankunan bakin iyakar sun sa kan dole jama’ar suka koma sansanin ‘yan gudun hijira. Suna da ‘yan uwa a sansanin. Dan abin da suke da shi suna rabawa a tsakaninsu. Wasu na sana’ar saida itace don samun abinda zasu kula da 'ya'yansu," a cewar Luka.
A watan Yunin shekarar 2014 ne Luka ya tsere daga jihar Bornon Najeriya bayan da 'yan ta'addan Boko Haram suka kashe sama da mutane 20 a kauyensu, ciki har da ‘yan uwansa.
Toudje Voumou, shi ne babban jami'in gwamnati a gundumar Mayo-Moskota, ya ce rundunar hadin gwiwa da ake kira MNJTF a takaice, ta kara yawan dakarunta a kan iyakar kasar. Rundunar dai na da dakaru daga Najeriya, Nijar, Kamaru da kuma Chadi.
Voumou ya ce kusan makonni biyu kenan ana gwabza kazamin fada tsakanin sojojin gwamnatin Kamaru da mayakan Boko Haram a bangaren kan iyakar na Kamaru da Najeriya. Voumou ya kuma ce an kafa sansanonin soja da dama domin tunkarar mayakan Boko Haram da ke fakewa a yankin suna muzgunawa farar hula a kauyukan da ke kan iyakar.
Rundunar dakarun MNJTF ta sanar a watan Fabrairu cewa za ta sadaukar da watan Maris domin murkushe sauran ragowar mayakan Boko Haram a yankin kan iyakar.