Jana’izar Shahararren Dan Wasan Kwallo Pele

Jami'an tsaro suna raka gawar Pele zuwa inda za a binne shi

Sabon shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, na daga cikin wadanda suka kai ziyarar girmamawa da ban-kwana a filin wasa na Vila Belmiro da aka yi jana’izar Pele.

A ranar Talata al’umar kasar Brazil take shirin binne fitaccen dan wasan kwallon kafar duniya Pele.

Pele, wanda asalin sunansa, Esdon Arantes do Nascimento ya rasu a ranar Alhamis bayan fama da cutar sankarar hanji. Shekarunsa 82.

Sabon shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, na daga cikin wadanda suka kai ziyarar girmamawa da ban-kwana a filin wasa na Vila Belmiro da aka yi jana’izarsa, wanda anan ne Pele kwashe tsawon rayuwarsa ta kwallo.

Yadda aka ratsa da gawar Pele cikin titunan garin Santos

An yi taron addu’o’i a filin wasan gabanin a dauki gawarsa wacce aka ratsa da ita ta titunan Santos da ya kasance mahaifarsa inda aka dangana zuwa makabarta.

Daga cikin wadanda suka halarci janai’zar har da aminin Pele, Manoel Maria, wanda tare suka buga kwallo a kungiyar Santos.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Gianni Infantino, ya fadawa manema labarai cewa, ya kamata kowacce kasa ta samu wani filin wasa ta saka sunan Pele.