A jamhuriyar Nijer hukumar saka ido akan sha’anin Ruwan sha wato ARSeau ta shirya taron kara wa juna sani da nufin jin ta bakin shugabannin kungiyoyin kare hakkin jama’a a game da tarin matsalolin da ake fuskanta a fannin ayyukan samar da Ruwan sha da kasuwancinsa a kasar ta yadda za a samar da mafitar mawuyacin halin da talakkawa ke ciki.
Wakilin muryar Amurka Souley Moumouni Barma ya aiko mana Karin bayani daga Yamai.
Ganar da al’umma ainahin aiyukan da suka rataya a wuyan hukumar ARSEau wace gwamnatin Nijer ta kafa a shekarar 2020 da nufin tsaka tsarin a sha’anin Ruwan sha ya sa shugabanin hukumar shirya wannan taro domin jin ta bakin jami’an kare hakkin jama’a a game da yadda suke kallon sha’anin Ruwan sha a kasar ta Nijer. Malan Garba Bawa Naroua shine shugaban majalissar saka ido akan sha’anin Ruwan sha wato Conseil National de Regulation du secteur de l’eau.
Tsarin biyan kudaden Ruwan sha a karshen wata wani al’amari ne da ke haifar da tada jijiyoyin wuya a wajen al’umma a yayinda samun ruwa akai akai a fomfuna a sabbin n’guwannin manyan birane ke zama babban jidali. Alhaji Hamidou Sidi Fody shine wakilin kungiyoyin fararen hula a hukumar ARSeau.
A karshen watan nan na disamba ne kwangilar saida Ruwan sha da gwamnatin Nijer ta ba kamfanin SEEN a shekarar 2001 ke kammala matakin da al’umma ta yi na’am da shi saboda kosawa da tsarin aiyukan wannan kamfani yayinda mazauna karkara ke zargin kananan kamfanonin saida ruwa da gasa masu aya a hannu.shugaban kungiyar CODDAE Alhaji Moustapha Kadi na cewa wannan taro dama ce ta ankarar da mahukunta abubuwan dake wakana.
Sanin tasirin aiyukan kungiyoyin fafutika akan maganar kwato hakkin jama’a ya sa Hukumar ARSeau ta bukaci goyon baya daga garesu a yunkurin da ta sa gaba.
A karshen wannan taro na wuni 1 hukumar ta ARSeau dake karkashin fadar fra minister za ta gabatar wa gwamnati takardun shawarwarin da aka tsayar yayinda ya zame wa kungiyoyin farar hula wajibi su zagaya illahirin jihohin Nijer don sanar da al’umma hanyoyin shigar da koke koke game da dukkan abubuwan dake da nasaba da toye hakkin akan maganar Ruwan sha.
Saurari cikakken rahoton Souleyman Barma:
Your browser doesn’t support HTML5