A wani yunkuri na kawo sassauci ga rayuwar mata da kananan yara musamman marayu da a halin yanzu matsalolin tsaro da talauci ya tilasta wa yin gararamba a kan tinunan Najeriya, an soma samun sauki ta fannin tallafi daga daidaikun kungiyoyi inda kungiyar izala ta bi sahu wajen aurar da wasu mata marayu marasa gata su 20 tare da basu tallafi na kudi da sama musu sana'ar yi.
Duk da cewa akwai dimbin kalubalen da ma’aurata ka iya fuskanta a zamnatakewarsu, Haj.Rabi Muhammad mai fafutukar kare hakkin mata kana shugaban kungiyar Domin Marayu ta ce ba su yi kasa a gwiwa ba wajen fadakar da amaren
Tabarbarewar tsaro, daya ne daga cikin matsalolin da Najeriya ke fama da shi, lamarin dake tilastawa mata da yara rayuwa a kan tituna kara zube, duk da kasancewarsu masu rauni, dalilin da ya sa ake cigaba da jan hakula ga masu hannu da shuni da gwamnati za su shigo wajen rage nauyin wallahalu da marayu marasa galihu ke fuskata wajen agaza musu.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5