Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta bada sanarwar dakatar da 'yan wassan kwallo na kasashe 2, daya, dan kasar Salvador Erick Alejandro Rivera (Salvador), da a ka gano ya sha kwayoyin kara kuzari a wasan da kasar sa ta shirya ran 8 Satumban 2021. Sai na 2 wato Sabri Ali Mohamed (Djibouti), da a ka gano shi ma ya sha ababe masu kara karfin jiki da hukumar ta duniya ta kwallon kafa ta hana ayi anfani da su a lokacin da kasarsa ta buga wasan kwallon kafa a ranar12 Nuwamban 2021.
FIFA ta zargi 'yan wasan da saba wa ka'idodinta a ayoyin kundinta masu lambobi 6 da 17 da su ka hana shan wadansu kalolin kwayoyi dake kasancewa masu kara guzari.
Tuni yan wasan suka shanye wani lokaci na takunkumin da FIFA ta saka musu da zai kare a ranakun 5 ga Oktoban 2025 da kuma 11 Yulin 2026.
Hukumar ta kwallon kafa ta duniya FIFA, ta ce, wannan dakatarwa, ta shafi wasannin kasa da kasa da na cikin gida da wadanda a ke yi a hukumance da ma na sada zumunci ta la'akari da aya mai lamba 30 ta dokokin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.
Ana tunanin cewa, tauraron kwallon kafa na duniya kuma na kasar Portugal Cristiano Ronaldo, zaif fice daga kulob din Man United, wata kila izuwa kulob din Athletico de Madrid na kasar Spain.
Kungiyar dai ta Man United, ta sha kashi so 2, a wasannin Firimiya Lik na kasar Britaniya, hasali ma kungiyar ba zata buga wasannin wannan shekara ta bana ba na Champions Lik na kulob kulob da suka kasance zakaru a kasashensu a Nahiyar Turai.
Daman, a baya bayan nan, manyan kungiyoyin kwallon kafa 2 na nahiyar Turai, sun so su daukin dan wasan inda suka yi masa tayi mai tsoka, amma cewar da dan Wasan yayi sai an bashi albashi na tsabar kudi Yuro har Miliyan 45, abinda ya tsoratar da manyan kungiyoyin Turai da su dauki dan wasan, cewa da Cristiano Ronaldo.
A wasan cikon gurbi na mako na 2 na kakar kwallon kafa ta Ingila, an tashi kunnan doki 1 - 1 tsakanin Liverpool da Crystal Palace.
Yanzu haka dai, kungiyar Liverpool tana matsayi na 12 da maki 2, yayin da Crystal Palace ke a matsayi na 16 da maki 1 kawai.
A karshen wannan makon, Liverpool zata ziyarci Man United yayin da Crystal Palace zata ziyarci Aston Villa.
Shi ko dan kwallon kafar nan na kasar Faransa, Benjamin Mendy da ke buga wa gefen hauni na bayan kungiyar kwallon kafa ta kasar Britaniya cewa da Man-City da ke bayyana tun ranar 10 ga watan Agusta a kotun Shester a arewacin Ingila, inda a ke zarginsa da laifuka guda 8 da suka shafi fyade, hasali ma abokinsa dan shekaru 41 mai suna Louis Saha Matturie shi ma ana zarginsa da yin fyade tsakanin ranakun watan Yulin 2012 da Agustan 2021, yayin da su kuma ababen da a ke zargin Benjamen Mendy da aikatawa sun faru ne tsakanin Oktoban 2018 Agustan 2021.
Saurari cikakken rahoton Harouna Mammane Bako:
Your browser doesn’t support HTML5