SOKOTO, NIGERIA - Wadannan rikice-rikicen na ci gaba da wanzuwa yayinda Jam'iyyun siyasa suka kasa warware wasu daga ciki, suka bar mabiya na cacar baki.
Masana kimiyar siyasa sun bayyana cewa samun rikici tsakanin jam'iyun siyasa ba bakon abu bane musamman idan lokutan zabe sun karato domin bangarori dake rikici da juna suna yi ne don kare muradin su.
To sai dai abinda kan ci gaba da daukar hankalin jama'a shine yadda jam'iyun ke kasa warware rikicin har wasu lokuta sai abin ya kai ga canjin sheka.
Jami'iyar APC wadda ke mulkin kasar ta tsinci kanta cikin rudani tun a lokutan zabubuka data gudanar na shugabannin ta a shekarar bara, kuma kawo yanzu ta kasa warware su, a wasu Jihohi.
Fiye da mako daya da ministan shara'a na Najeriya Abubakar Malami SAN ya furta wani kalami akan ja-in-ja da ake yi akan shugabancin jam'iyar na jiha, a jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya duk da yake batun yana gaban kotu.
Wannan kalamin ya bar baya da kura tsakanin ‘ya'yan jam'iyar inda suka shiga mayar da martani, sun cewa an kai wa kotu sai a dakata a gani.
Har Ilayau gamayyar kungiyoyin jam'iyar APC karkashin dayan bangaren dake jayayya karkashin jagorancin Isa Jabbi sun kalubalanci dayan bangaren.
Su kuma zababbin shugabannin APC a kananan hukumomi 23 na jihar karkashin jagorancin Muhammad Musa sarkin Alaru sun bayyana cewa, yau she aka zauna balle a samu daidaito.
To ko yaya mashar'anta ke kallon wannan lamari da yaki ci yaki cinyewa. Barrister Mu'azu Liman yabo masanin dokokin kasa ya bayyana cewa, maganar jam’iya tayi shiru zai zama illa, dole ne jam’iya ta dauki mataki.
Yanzu jama'a sun zura idanu su ga yadda za ta kaya ga sauran rikittan da aka kasa warwarewa watanni da dama kuma ga lokaci na kara matsawa ga lokutan zabubuka.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5