Dan takarar shugaban kasar Amurka na jam'iyyar Democrat Joe Biden, a fitowarsu tare ta farko da Sanata Kamala Harris mataimakiyarsa

Your browser doesn’t support HTML5

Joe Biden, ya bayyana kafa babban tarihi, a yayin da yake gabatar da Sanata Kamala Harris, wadda ya zaba a zaman mataimakiyarsa a gangamin yakin neman zabe. Biden da Harris da dukan su suke sanye da takunkumin rufe fuska sakamakon annobar coronavirus, sun yi jawabai a dandalin wani taro.