Shirin Kirsimeti A kasar Amurka

Your browser doesn’t support HTML5

Kirsimeti lokaci ne na bukin tunawa da haihuwar Annabi Isah Almasihu da mabiya addinin Krista ke yi. Kamar wasu kasashe, wannan lokaci ne da Amurkawa ke kawata wurare da kwalliya, lokaci ne kuma na bada kyaututtuka.
A wannan lokacin ma gwamnatin kasar na kawata wasu wuraren shakatawa don masu zuwa ziyara, kamar wani lambu da ake kira Botanical Gardens a birnin Washington DC.