Za Mu Cigaba Da Tura Matasa Karatu Kasashen Waje- In Ji Kwankwaso

Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

A ranar Talatar da ta gabata ce wasu rukunin daliban jihar Kano su fiye da 200 su ka tashi zuwa kasar India domin karatun digiri na biyu a jami'o'in kasar kuma a fannoni daban daban.

Gidauniyar Kwankwasiyya ce ta dauki nauyin daliban bayan neman gangamin kaddamar da neman tallafawa asusun gidauniyar a kwanakin baya.

Shugaban Gidauniyar Kwankwasiyya, Tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce halin da suka samu kansu a cikin Najeriya musamman ma jihar Kano shi ne suka ga bai kamata su nade hannayen su ba su ja da baya su boye a karkashin gado ba su rafke yau babu dadi kuma wannan yasa gobe kuma ta kasance babu dadi ba.

Ya kuma kara da cewa shi yasa suka hadu a jihar Kano suka yi shawarwari da abokai da yan uwa cewar me ye mafuta.

Mafitar dai abubuwa ne masu yawan gaske ka iya cewa firamare, sakandare da kuma makarantun gaba da sakandare duka akwai matsaloli da sauransu, to duk wannan karshen ta idan kayi lissafi babu abinda zaka iya, saboda haka sai suka tsaya suka ga cewa wadannan matsaloli da yawa.

Bayan da suka tsaya suka duba sai suka ga cewa bari su dauki na saman, matasa wadanda sun nuna cewa su jarumai ne akan ilimi domin su je kasashen waje domin su karo karatu su kuma sadu da mutane mabanbanta masu kala daban da masu yare daban da su da kuma addinai daban daban da al’adu daban, kuma mutane daruruwa ne suka nema amma suka tace mutane 370 kafin daga bisani suka kara tacewa suka koma 242, a cewar Kwankwaso.

Ci Gaba Da Tura Dalibai Kasashen Waje

Kwankwaso ya ce duk wani mutumin kirki da yake aikin alkahairi so yake ya ci gaba da wannan aiki, kuma burinsu shine su ci gaba kamar yadda yanzu suka debi 'yan Kano da za su gwada su don su ga yadda nasarar su za ta fito.

Sannan za su duba idan da hali za su buda suga koda daga arewa maso yammacin Najeriya su debo matasa irinsu su sake turawa, kuma sun sami hadin kai sosai a Kano yadda jama’a suka bada kudi a hannu wasu kuma suka sayi kati suka tura ta waya zuwa cikin asusun Gidauniyar Kwankwasiyya.

Shugaban Gidauniyar ya ce sun kashe kudade da yawa kuma dukkan kudaden da suka kashe za su ci gaba da kashewa, za kuma su ci gaba da bawa daliban kudaden tallafi wadanda basa cikin kudaden makaranta da suka biya musu wanda za su ringa siyan sabulu wanka da sauransu da bay a cikin kudaden da muka biya.

Daga bisani shugaban Gidauniyar ya yi kira da mutane da su tallafawa wannan asusu domin har yanzu a bude yake, ya kuma yi kira ga shugabanin jami’o’i da ma’aikatar ilimi da su shigo da ilimi mai saiti wanda idan yaro ya gama makaranta bazai tafi yana neman aiki ba akan titi kamar yadda suke gani a halin yanzu.

Saurari cikakkiyar hirar da wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya yi da Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso:

Your browser doesn’t support HTML5

Kwankwaso- Za Mu Ci Gaba Da Tura Matasa Karatu Kasashen Waje