Majalisar dattijai ta kada kuri’a jiya alhamis da ‘yan majalisa sittin da biyar suka amince, talatin da hudu kuma suka ki amincewa, da zai sabunta dokar harkokin leken asiri na kasashen ketare lamba da dari bakwai da biyu da ake kira FISA na tsawon shekaru shida.
‘Yan majalisar sun kada kuri’ar goyon bayan sabunta shirin makon da ya gabata. Ana kuma kyautata zaton Shugaba Donald Trump zai sa hannu a kai yau jumma’a.
Sashe na dari bakwai da biyu na dokar ya ba cibiyoyin leken asirin Amurka hurumin su saurari da kuma karanta sakonnin da ake aikawa daga kasashen ketare ta hanyoyin sadarwar zamani na dandalin kamfunna irin su Facebook, Google, da kuma Verizon domin tattara bayanai kan ‘yan kasashen ketare da ake sawa ido.
Jami’an leken asirin Amurka sun jima suna bayyana shirin a matsayin mai matukar muhimmanci, suka ce, sun sami bayanai da dama ta wannan hanyar da suka taimaka wajen dakile ayyukan ta’addanci.