A cigaba da hada hadar ‘yan-wasan kwallon Kafa ta duniya na watan Janairun dubu biyu da sha takwas. Kungiyar kwallon Kafa ta Borussia Dortmund ta ce a shirye take ta bar danwasan gabanta Emerick Aubagmeyang da ya koma kungiyar Arsenal.
Inda ta bukaci dauko danwasan gaba na Batshuayi mai shekaru 24, dan ya maye gurbin sa, danwasan Arsenal Alexsi Sanchez, ya amince da ya dawo kungiyar Manchester United bisa yarjejeniya kwantirakin shekaru hudu da rabi da kungiyar ta Manchester United.
Alexsi zai amshi fam miliyan £14 a shekara daga United, Inda duk sati yana iya karban fam dubu £400 a matsayin albashi. Sai dai yanzu Sanchez yana jiran yadda zata kaya tsakanin Arsenal, da danwasan Manchester United Mkhitaryan, wanda kungiyar ta Arsenal ta bukaci a sanya shi cikin cinikin.
Sai dai shima Mkhitaryan yace yana bukatar Arsenal ta amince da bashi albashi feye da wanda yake karba a Manchester United fam dubu £150 duk sati kafin ya amince.
Real Madrid tace yanzu lokaci yayi da ya kamata ta sayi ‘yan-wasan gaba, Inda ta nuna sha'awarta na dauko danwasan PSG Neymar Eden Hazard, na Chelsea da kuma Robert Lewandowski daga kungiyar Bayern Munich.
Napoli tana sha'awar dauko mai tsaron raga na Liverpool dan kasar Belgium maisuna Simon Mignolet, 29 wanda har yanzu bai sami kansa a kungiyar ta liverpool ba.
Westbromwich ta saka fam miliyan £12 wajan sayen danwasan tsakiya na Fulham kuma Kaftin a kungiyar maisuna Tom Cairney. Inda take yunkurin karawa zuwa fam miliyan £15 din ganin ta dauko shi.
Juventus tana zawarcin danwasan baya na Arsenal Hector Bellerin, inda tace tun shekara 2014 take sha'awar ganin ta dauko danwasan 22, har ila yau kungiyar ta Juventus tana bukatar dauko danwasan tsakiya na Tottenham Christian Eriksen, 25 ko kuma Mesul Ozil na Arsenal don su kasance mata sabin lamba goma a kungiyar, Chelsea tabi sahun Manchester City wajan zawarcin danwasan tsakiya na Nice maisuna Jean-Michael 26.
Westham tana bukatar ganin ta dauko danwasan tsakiya na Inter Milan Joao Mario da gaggawa a matsayin aro. Ganin cewar danwasan yanzu haka baya samun kansa a kungiyar ta Inter, Shi kuwa danwasan gaba na Westham Javier Hernandez, na shirin barin kungiyar ne don komawa kungiyar Besiktas don taka leda.
Tuni dai kungiyar ta turo wakilanta don tattaunawa da danwasan 29, kan batun, haka kuma Kungiyar ta Besiktas ta kasar Turkiya tana zawarcin danwasan gaba na Leicester City Islam Slimani.
Inda a ranar Talata shugaban Kungiyar Fikret Orman yana filin wasa na King Power dan ganin yadda danwasan yake taka leda.