Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya gayawa wani taron ministocin harkokin kasashen waje na kasashe akalla 20 da suke taro a Canada cewa, fasinojin wani jirgin sama daga birnin San Francisco zuwa Hong kong, sun ga makami mai linzami mai ratsa nahiyoyi da Koriya ta Arewa ta harba cikin watan Nuwamba.
Sakataren wanda yake magana a taron a jiya Talata, wanda aka shirya da nufin hada kai domin kara tunkarar Koriya ta Arewa, yace wannan ya nuna irin gangancin gwamnatin Kim Jong Un.
Kamar yadda hukumar zirga zirgar jiragen sama ta Amurka ta bayyana akwai ratar ta kai kilomita 500 daga inda makamin ya dira, kuma akwai wasu jiragen fasinja kamar guda tara a yankin, wanda hakan yana da matukar hadari.
Sai dai Sakatare Tillerson bai bayyana wani kamfanin jirgin sama na fasinja ne ya hangi makamin ba.