Shekarun mutane a fadin duniya na karuwa, fiye da yadda ake mutuwa da wuri a da, mutane na kara yawan shekaru kafin mutuwa, hukumar lafiya ta duniya, ta bayyana cewar yawan tsofaffi da ke rayuwa da kansu a fadin duniya sun karu, kuma hakan abun damuwa ne.
Mutane da yawa basa daukar dawainiyar iyayensu a lokacin da suka kai shekarun tsufa, musamman ‘yan zamani matasa. Don magance matsalar kadaici, da halin damuwa da tsofaffi ke shiga a lokacin rayuwar tsufansu.
Wani kamfanin kasar Isra’ila ya kirkiri mutun-mutumi mai suna ‘Elliq’ wanda aka kirkre shi don taimakama tsofaffi yayin da suke cikin lokacin kadaici a rayuwar su, kasancewar basa zama tare da ‘ya’yansu ko ‘yan’uwa da ka iya taimaka musu wajen more rayuwar su ta tsufa.
Elliq, na’ura mai kwakwalwace da zata rika taya tsofaffi fira, a duk lokacin da suke cikin halin kadaici, ko dai na’urar ta basu labarin nishadi, ko labarin da zai tuna musu wasu abubuwa da zasu manta da damuwar su.
Haka na’urar zata gaya ma tsoho ko tsuhuwa wasu abubuwa da ya kamata suyi, wanda suka sabayi, kamar motsa jiki, bacci, cin abinci, shan ruwa da dai makamantan su.