Alkalumma sun bayyana dinbin kudade da suka salwanta, sakamakon ambaliyar ruwa da aka samu a jihar Texas ta kasar Amurka. Ambalaiyar ruwa guda uku da aka samu a shekarar da ta gabata a kasar Amurka, ta zama kangaba wajen lakume dukiyoyin al’umma.
An kiyasta asarar da aka tabka har sau 16 a shekarar 2017 da kudin su ya kai kimanin dallar Amurka billiyan $306 kwatankwacin sama da Naira tiriliyan dubu daya da dari daya.
Ambaliyar da akaima lakabi da ‘Hurricane Harvey’ ta lamukume dukiya fiye da kowacce, wadda ta lashe wasu bangarorin jihar Texas, wadda ita kadai ta lashe dukiya fiye da dallar Amurka billiyan $125, wanda idan aka kwatanta da guguwar Katrina, ta shekarar 2005 da itama tayi barna matuka, sai guguwar Irma da Maria, sun lakume kimanin dallar Amurka billiyan $140.
Ita kuma gobarar daji da aka samu a jihar California, ta lakume kimanin dallar Amurka billiyan $18.