Kamfanin Wayoyin Blackberry Zai Kera Motoci Masu Tuka Kansu

Kamfanin wayoyi na Blackberry tare da hadin gwiwar kamfanin Baidu na kasar China, sun rattaba hannu akan wata yarjejeniyar kera motoci masu sarrafa kansu.

A jiya ne kamfanonin biyu suka cinmma wannan yarjejeniyar, hakan ya karasa kamfanin na Blackberry ya kara sa hannu da kamfanin Qualcomm, da Aptiv, kamfanonin dai zasu hada kai wajen kera na’urori da za’a daura cikin motocin don tuka kansu.

Kamfanonin dai na sa ran fara samun kudaden shiga daga shekara mai zuwa 2019, masu hannun jari da masana na bibiyar wannan yunkurin, wanda za’a yi amfanin da wasu na’urorin kwamfuta wajen hadawa da sarrafa motocin.

Wannan wani babban yunkuri ne, musamman ga kamfanin na Blackberry, domin kuwa kasuwancin wannan motar a baki daya kasuwanin duniya ne, a cewar Mr. Todd Coupland na kamfanin kasuwanci na Capital.