Ma'aikatar tsaron Amurka, Pentagon, ta fito a ranar asabar tana fadin cewa a karshen shekarar 2012, ta dakatar da shirin da ta jima tana boyewa duniya shi na binciken ko wasu halittu ko na'urorinsu daga wata duniya dabam a sararin subhana, sun taba zuwa nan doron duniyar bil Adama.
Sai dai kuma, ma'aikatar ba ta fito ta ce ta daina binciken wannan lamarin karkashin shirin nata mai suna "Advanced Aviation Threat Identification Program" ba tun da aka dakatar da ware kudi na musamman don shirin shekaru biyar da suka shige.
Jaridar New York Times ta ce wannan shiri na sirri na binciken rahotannin da mutane ke bayarwa na ganin wani abu da ba a sani ba yana yawo a sama, ko UFO a takaice, an gudanar da shi daga 2007 zuwa 2012. Dala miliyan 22 da aka kebe don gudanar da wannan shiri kowace shekara, yan aboye cikin dubban miliyoyin dalolin da ake warewa kowace shekara domin ma'aikatar tsaron.
Sai dai kuma duk da wannan ikirari, masu goyon bayan shirin sun ce har yanzu yana nan, kuma jami'ai suna binciken duk wani rahoton da sojoji, musamman ma na sama, suke bayarwa cewa sun ga wani abu da ba su saba gani ba a sararin samaniya.
A bayan wata tambayar da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gabatar mata, ma'aikatar tsaron ta fito a fili a karon farko ta yi magana kan wannan shiri, inda mai magana da yawun pentagon, Laura Ochoa ta fada cikin wani sakon Imel cewa "Wannan shirin ya daina aiki a cikin shekarar 2012. An yanke shawarar cewa akwai wasu batutuwan da suka fi muhimmanci da ya kamata a kashe kudi a kansu, don haka aka karkata kudi daga wnannan shirin."
Sai dai kuma, Ochoa ta kara da cewa "Ma'aikatar tsaro tana bayar da muhimmanci ga duk wani abu da ya kasance barazana ko kuma zai iya zama barazana ga mutanenmu, ko kadarorinmu, ko ayyukanmu. Muna daukar mataki a duk lokacin da muka samu bayani mai tushe."
Ma'ana dai, watakila har yanzu ma'aikatar ta Pentagon tana ci gaba da bin sawun irin wadannan rahotanni da mutane ke bayarwa cewa sun ga wani jirgi daga wata duniya ya sauka ko ya wuce ta wuri kaza da makamantansu.