Za'a Haramta Amfani Da Motoci Masu Shan Mai A Birnin Paris

Nan da ‘yan shekaru kadan, kukan mashin ko motoci zasu zama abun tarihi a cikin birnin Paris. A wani sabon yunkuri da mahukunta a kasar Parin, suke kokarin ganin an cinma nan da shekarar 2030.

Mahukunta a kasar na ganin cewar, ana samun karuwar matsalar dumaman yanayi da karuwar hayaniya, a cikin garuruwan su idan akayi la’akari da yadda motoci ke kai kawo.

Don magance matsalar ta dumaman yanayi, an fitar da sabon kuduri da zai samar da motoci masu aiki da hasken rana, ko caji kadai za’a dinga amfani dasu a kasar daga nan zuwa shekarar 2030.

A cewar shugaban karamar hukumar ta Paris Mr. Anne Hidalgo, idan Allah ya kai rai shekarar 2024, babu wata mota mai amfani da fetur ko man gas da zata kara shiga cikin garin. A lokacin da ake sa ran gudanar da wasannin Olympics.

A cewar mataimakin shugaban karamar hukumar, sun samar da duk wasu tsare-tsare da suka kamata a samar, don ganin an rage cinkoson motoci a birnin, da rage yawaitar karan ingina, kana da kananan cututuka da motoci masu amfani da mai ko gas kan haifar.

Ya kara da cewar, mafi akasarin mutane mazauna birnin basu da motoci, amma suna da sha’awar samun daya, wanda hakan zai kara sa garin cikin rudani, idan akace kowa yana da nashi abun hawan. Yadda za’ayi maganin dumaman yanayi, shine kawai a samar da motoci da basa amfani da mai.