Rahoton Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyanar da cigaba mai yawa, wajen yaki da cuta mai karya garkuwan jiki HIV/AIDS. Rahoton da aka fitar ‘yan kwanaki kadan kamin bukin ranar kanjamau ta duniya.
Ya tabbatar da cewar akwai maganin kanjama’u da mutane zasu yi amfani da shi don rabuwa da cutar. Kana mutane masu dauke da cutar zasu daina yadata ga sauran mutane.
Rahoton ya bayyanar da cewar akwai mutane sama da milliyan ashirin da daya, da suke dauke da cutar suna karbar magani, kimanin rabin adadin mutane masu dauke da cutar kenan. Hukumar dai na yunkurin kawo karshen cutar a fadin duniya nan da shekarar 2030.
Dr. Anthony Fauci, ya fara binciken maganin cutar tun a shekarar 1980, jim kadan bayan bayyanar cutar. Yace mutane dake dauke da cutar zasu iya koma ma rayuwar su kamar kowa. Musamman idan suna cigaba da shan magungunan su.
Likitan dai yayi suna a duniya, wajen binciken maganin cuta mai karya garkuwar jiki, kuma tson jami’in Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyanar da cewar yanzu haka muna da maganin cutar AIDS.
Ya kara da cewar “Ina nufin cewar akwai binciken kimiyya da ya tabbatar da karshen wannan cutar mai hallaka jama’a,” domi kuwa a ‘yan shekarun baya muna da magunguna masu karfi, wanda suke taimakama masu dauke da cutar.
Yanzu haka dai magungunan zasu taimaka wajen kare mutane marasa cutar kamuwa da ita, koda kuwa sunyi mu’amala da masu dauke da cutar, haka mutane na iya shan wasu kwayoyi don samun garkuwa daga daukar cutar daga masu dauke da ita a kowane lokaci.