Amurka Ta Ce Zata Ci Gaba da Kare Korea Ta Kudu Daga Barazanar Korea Ta Arewa

Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis yace babu wani abin da ya sake a shirin Amurka na bada kariya ga Korea ta Kudu game da barazanar makaman nukiliya da masu lizzami daga Korea ta Arewa.

Da yake jawabi ga rundunar sojin hadin gwiwar Amurka da Korea ta Kudu a yau Juma’a a kauyen ruce dake yankin Panmunjon inda Korea ta Kudu ke hadewa da ta Arewa, Mattis yacenmuna iya bain kokarinmu wurin warware wannan lamai ta hanyar diplomasiya, yana nufin batun shirin makaman nukiliyar Korea ta Arewa.


Mattis ya Ambato kalaman sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson yana cewar, ba manufrmu ce yaki ba, ya kara da cewar bukatarmu ce mu tilastawa Korea ta Arewa da dakatar da shirin makaman nukiliyarta da yake kara kaimi tun lokacin da shugaba Donald Trump yah au mulki.


A ziyararsa ta wuni biyu a Korea ta Kudu, Mattis ya gana da shugaba Moon Jae-in, a yu Juma’a kuma ya gana da manyan jami’an tsaron Amurka da kwamandodin sojan Amurka masu hannu kai tsaye wurin kawar da ayyukan Korea ta Arewa.