Wasu kadan daga cikin abubuwan ban sha’awa da sabuwar wayar ‘Google Pixel 2’ wadda ake sa ran idan Allah, ya kai rai ranar Alhamis mai zuwa za’a kaddamar da ita. Wayar na dauke da wasu sababbin salo, da babu wata waya a wannan karnin da ke da.
Duk dai da cewar wayar bata da wani kyau da yafi na sabuwar wayar iPhone, ko Samsung Galaxy amma tana dauke da wasu manhajoji da su kafi na sauran wayoyin. Wayar na dauke da tsarin da zai ba mutane damar shiga shafin na google don gudanar da bincike cikin sauri da sauki.
Sabuwar wayar tana dauke da sabon tsarin da idan mutun yana son bincike akan wani abu, ba sai ya rubuta ba, abu da kawai mutun zaiyi shine, ya haska kyamarar wayar ta kalli hoton abun, daga nan wayar zata bada bayanai da suka shafi abun da ta gani.
Haka wayar zata gaya maka sunan duk wasu gine-gine, ko shaguna da suke kusa da hanyar da kake bi, batare da mutun ya bace ba wajen neman wani wuri. Haka idan ka kusanci wasu shaguna, wayar zata kawo maka adireshin yanar gizon shagunan, da lambar wayoyin su idan kana da bukata sai dai kawai ka danna don magana.
Kamfanin google, sun bada tabbacin cewar sabuwar wayar za tayi dai-dai da duk wani abu da abokan hurdar su ke bukata, domin kuwa wayar zata wuce tsara a jerin layin wayoyin zamani, musamman a wannan karni na ashirin da daya da ake ciki.