Shafin Facebook ya zamanto dandalin sada zumunci ga miliyoyin mutane shekaru masu yawa, sai dai abin bakin ciki shine a ‘yan shekarun nan ana amfani da fasahar tabbatar da lafiyar mutane a lokacin da wata masifa ta afkawa yankinsu.
Masu shafin Facebook na yin amfani da fasahar ne wajen tabbatarwa da ‘yan uwa da abokan arziki cewa suna nan lafiya babu wani abu da ya same su a duk lokacin da wata annoba ta afkawa yankinsu, kamar harbin mai uwa dawabi da girgizar kasa da kuma mahaukaciyar guguwa.
Bayan da Stephen Paddock mai shekaru 64 ya bude wuta kan dubban mutanen da suka je kallon wasan mawaka a daren ranar Lahadi, inda ya kashe mutane 59 da kuma raunaka wasu 527.
Facebook ya bude wannan fasahar da mutane suka yi ta amfani da ita wajen tabbatarwa da ‘yan uwa da abokan arziki halin da suke ciki. Haka kuma Facebook yayi ta kokarin saka labarai da hotunan abin da ke faruwa a Las Vegas.
Da kuma gargadin mutane da su guji yankin da lamarin ya shafa domin ganin an taimaka wajen kare yawan asarar rayuka.
Your browser doesn’t support HTML5