'Yan sanda a Las Vegas dake Jihar Nevada a Amurka, sun ce wani mutum ya bude wuta a kan masu halartar wasan mawaka na kaboyi cikin daren lahadi, ya kashe mutane akalla hamsin, tare da raunata wasu fiye da dari hudu, a wannan harin bindiga da ya zamo mafi muni a tarihin Amurka.
Baturen 'yan sandan birnin Las Vegas, Joseph Lombardo, ya shaidawa 'yan jarida cewa maharin wani dattijo ne mai suna Stephen Paddock, dan shekaru 64 da haihuwa daga garin Mesquite a Jihar ta Nevada. Dan bindigar ya bude wuta kan mutane fiye da dubu 22 dake kallon wasan mawakan daga dakinsa dake hawa na 32 na wani hotel mai suna Mandalay Bay Casino, wanda ke tsallaken hanya daga filin da ake gudanar da wannan wasa. Hotunan bidiyo sun nuna wadanda suka je kallon wasan suna rugawa da gudu, wasu na neman wurin buya, wasu kuma na ihu a yayin da aka yi ta jin karar bindiga.
Lombardo yace zaratan ‘yan sanda na rundunar SWAT, sun kiutsa cikin dakin dan bindigar suka same shi a mace. Yace sun yi Imani Paddock shi ya kashe kansa. An samu makamai da dama a dakin nasa.
Yace ba su san dalilin Paddock na bude wutar ba.
Hukumomin sun kuma yi farautar wata mace da aka ce suna tare da Paddock domin nerman karin bayani. Jami'in 'yan sandan yace an same ta. Daga bisani, ‘yan sanda sun bayar da wata sanarwa suka ce babu hannunta a wannan lamarin, kuma Paddock shi kadai suke kyautata zaton ya kitsa ya aikata wannan abu.