Matasa 'Yan Kasashen Waje Na Farfado Da Wasan Kwallon Kwando A Duniya

Bayan wasan tamola, wasan kwallon kwando ‘Basketball’ na kara zama wasa da ke shiga cikin ra’ayoyin matasa a fadin duniya. Wasan kwallon kwando a kasar Amurka na kara shiga cikin jerin wasannin da su kayi fice a duniya.

Kungiyar kwallon kwando ta kasa a Amurka nada ‘yan wasa 113, wanda kashi daya 1% cikin uku 3% na matasan, sun fito daga wasu kasashe a fadin duniya ne. Kasashen sun hada da kasar Poland, kasar Czech Republic, sai kasashen Afrika.

A cewar daya daga cikin ‘yan wasan Ian Mahinmi, wanda mahaifiyar shi ta fito daga kasar Jamaica, kana mahaifin shi kuwa dan asalin kasar Benin ne, a yankin Afrika maso yamma. Matashin mai shekaru 28, yace wasan kwallon kwando wasa ne da yake da muhimanci ga lafiyar matasa.

Kuma wasa ne da zai ba matasa damar iya dogaro da kai, domin kuwa mutun zai samu kudi matuka, idan har yana da hazaka wajen maida hankali, domin wasa ne da kawai yake bukatar sanin makama da duk dubaru.

Hakan yasa yanzu ya daukar ma kanshi cewar, duk shekara zai dinga ware wasu watanni don zuwa kasashen Afrika, da zummar koyar da dubarun wasan kwallon kwando. Yana ganin cewar akwai matasa da suke da basira ‘yan kasashen Afrika da ake da bukatar su a fagen wannan wasan.

Domin wasa ne da yake bukatar matasa masu tsawo, lafiyar jiki, da kuma sha’awa. Haka shima kocin wata kungiya mai suna Washington Wizards, ya bayyanar da irin bukatar da ake da ita, na samun ‘yan wasa da suka fito daga kasashen Afrika.

Domin ya zuwa yanzu yaga matasa daga wasu kasashe, da suke taka muhimmiyar rawa a fanin wasan kwallon raga. Don haka yana kara bama matasa kwarin gwiwa, da su tashi tsaye wajen shiga wasan basketball kamar yadda suke sa kansu cikin wasan tamola.