Aliyu Lawal Aliyu, dan asalin jihar Katsina ne, wanda ya samu damar kammala karatun shi, tun daga firamari har zuwa digirin farko duk a kasar Najeriya. Bayan kammala bautar kasa 2011, a jihar Cross River Calabar. Yayi aiki da kamfanin sarrafa kasa da ma’adananta, da ake siminti ‘United Cement (UNICEM) wanda ke karamar hukumar Akampa, a wani yanki na jihar ta Cross River.
Ya kuma samu damar zuwa kasar Birtaniya, wajen karin karatu a matakin digiri na biyu, a fannin ‘Telecommunication Enginnering’ sadarwar zamanin, da sanin yadda ake kera waya, da sada sakonni waya da hada yanar gizo daga gari zuwa wani gain ko kasa zuwa kasa.
Daga bisani kokarin Aliyu, yasa jami’ar Sunderland dake babban birnin Birmingham, a kasar Birtaniya, sun bashi gurbin kara karatu, a matakin digirin digirgir, batare da biyan ko sisi ba. Wanda yanzu haka yake kokarin kammalawa.
A iya fahimtar Aliyu, Ilimi a wannan zamani ya zama wajibi ga kowane matashi, saboda ginshiki ne na rayuwa, lokaci ya kai wanda hatta kasuwancin, da ake yi yanzu yafi bunkasa idan aka hada da ilimi. Kuma ya zama nauyi da amana ga shuwagabanni, hakimai, masu unguwanni, da su tashi tsaye domin nemar ma matasan su yanci ta hanyar ilimi.
Ilimi yana taimakon mutun ya fita daga wani yanayi na talauci da kara basira, dan tafiyar da rayuwar mutun. Yawancin matasa suna ganin bata lokaci ne a tsaya kusan shekaru goma shabiyar, tun daga firamare har jami’a ana abu daya. Batare da la’akari da alfanun da ka iya biyo baya ba.
Don haka wannan kalu bale ne ga duk wani matashi da ya tashi wajen neman ilimi a kowane hali, ta haka ne kawai za’a iya samun tattalin arziki mai daurewa, idan matasa nada ilimi da zuciyar taimakawa wajen ciyar da kasa gaba.