Facebook Zasu Yada Wasannin Cricket Na Kasar India Kai Tsaye A 2022

Kamfanin Facebook sun doke sauran abokan hamayyar su, wajen kokarin samun damar watsa shirye-shiryen wasannin ‘Cricket’ na kasar India kai tsaye. Cikin jerin kamfanonin da suka nemi wannan damar basu samu ba, kamfanin na facebook sun lashe damar da tsabar kudi da suka kai dallar Amurka billiyan $600.

Wannan wata damace da shafin facebook zasu watsa wasanin a dai-dai lokacin da ake gudanar dasu kaitsaye, a koina a fadin duniya. Wannan wasan na criket shine wasa da yafi karbuwa a kasar India. Masu sha'awar wasan zasu iya kallon wasan a koina suke a duniya ta shafin facebook nasu.

Nasarar dai na kara nuna yadda kamfanin na facebook, suke a shirye don gabatar da duk wasu shirye-shirye da ake gudanarwa a kafofin gidajen talabijin. Haka zai kara tabbatar da cewar, facebook ko kafar sadarwar yanar gizo, zasu iya doke gidajen jaridu musamman na talabijin nan bada jimawa ba.

Domin kuwa duk wani labari da mutun ke nema, zai iya samun shi a koina yake matukar yana da yanar gizo. Mutane da yawa a fadin duniya zasu kara kashe lokaci mai tsawo a shafin na facebook, idan har suna samar da labarai na talabijin.

A shekarar da tagabata ne suka fara gabatar da watsa wasannin kai tsaye, lokacin da kungiyar Manchester United suka gwabza da kungiyar Everton. Tun daga wannan lokacin suke yada wasanin kwallo mai raga ‘Basketball’ da kwallon ‘baseball’