Labari daga majiya kwakkwara na bayyana cewar, dan sarauniyar Ingila, Yarima William da maidakin shi Duchess, suna shirye-shiryen taron sabuwar jaririya, da zasu haifa ta uku. A cewar fadar saraniyar ta Kensington, amaryar yarima Kate, bata jin dadi, wanda hakan yasa bazata halarci wani taro ba, biyo bayan laulayi da takeyi.
Sarauniyar Ingila da dangin Kate, sun nuna jin dadin su matuka da wannan sabuwar jaririyar, yarima da matar shi masu shekaru 35, da haihuwa suna da yara biyu, Yarima George mai shekaru 4, sai kanwarshi Charlotte, mai shekaru 2.
Gidan sarauniyar na murna da farinciki, na wannan baiwar da Allah yayi musu, inda suke kokarin ganin Yarima George ya fara zuwa makaranta a ranar Alhamis mai zuwa. Ya zuwa yanzu dai ba’a tabbatar da ranar da ake tsannmanin haihuwar sabuwar jaririyar ba.
Har dai anfara rade-radin sunan da ake sa ran za’a sama jaririyar, wanda ake sa ran za’a sakama sunan margayiya mahaifiyar yarima Williams ‘Prince Diana’ ganin cewar a ‘yan kwanakin bayane akayi bukin tunawa da ita bayan cikarta shekaru 20 da rasuwa.