A ranar Laraba ne idan Allah, ya kai rai gidan abincin Domino’s Pizza, zasu kaddamar da sabon salon isar da sakon pizza ga abokan hurdar su, wajen amfani da mota mai tuka kanta don isar da sako. Wannan sabon tsarin, zai magance yadda mutane ke kwankwasa kofar gidajen mutane, da kuma kawo karshne bada abun goro.
Gidan abincin tare da hadin gwiwar kamfanin kera motocin Ford, suka samar da tsarin, abu kawai da mutun yake bukata, bayan siyan abinci ta amfani da yanar gizo, shine ya rike wasu lambobi guda 4 da za’a bashi.
A duk lokacin da motar ta isa gidan mutun zai fito, don danna lambar a jikin motar, gilashin baya zai bude, sai mutun ya dauki sakon shi. Za’a fara gwajin ne a birnin Ann Abor, wanda yake garin asalin gidan abincin na Domino’s Pizza.
Tsarin gwajin zai ba kamfanonin biyu, damar ganin yadda mutane zasu gudanar da mu’amalar su, da motar mai tuka kanta. Kamfanin dai kan kai sakon pizza, gidajen mutane sama da billiyan daya a fadin duniya, a duk inda suke.
Amma wannan sabon tsarin zai saukaka yadda mutane ke tuka mota, don kai sakon pizza gidajen mutane. A cewar kamfanin Ford, suna kokarin samar da motoci, masu tuka kansu nan da shekarar 2021, don haka yasa suke hadin gwiwa da kamfanoni don sanin yadda suke bukatar motar, sai su kera ta yadda zata biya bukata.