Ana Zargin Kamfanin Apple Da Cire Manhajar VPN A Kasar China

Kamfanin Apple, sun bayyanar da kudirin su na cire tsarin manhajar VPN a wayoyin da suke hadawa a kasar China, hakan ya biyo bayan umurnin gwamnatin kasar China, na neman a cire tsarin.

Shi dai tsarin VPN yana bama mutun damar aikawa da samun damar shiga yanar gizo da asusun mutun ‘Account’ na kamfanin da mutun yakema aiki, batare da wasu sun samu damar shiga cikin tsarin don ganin abun da mutun yake aikiwa ba.

Gwamnatin kasar ta China, ta umurci kamfanonin hada wayoyin hannu, da su cire wannan tsarin a wayoyin su, domin tana so ta dinga bibiya ga yadda mutane ke gudanar da mu’amalolin su, tsakanin kanwunan su da kamfanonin da sukema aiki.

Da yawa wasu wayoyi da aka kera a wasu kasashe, idan aka kaisu kasar China, mahukunta a kasar basu samun damar shiga cikin tsarin wayar don ganin abun da mutun ya keyi.

A sakon da kamfanin na Apple suka fitar, dake bayyanar da kudurin su cewar, zasu cire manhajar, domin kuwa gwamnatin ta umurce su da suyi hakan a farkon wannan shekarar.

Sun kara da cewar, wannan babban abun ki ne, da gwamnatin ta fitar, wanda ba zaibama ‘yan kasa damar boye wasu sirrikan suba. Wasikar ta kara da cewar, zamu cigaba da bin umurnin gwamnatin kasar China, duk da cewar wannan dokar ta taka hakkin dan’adam na sirri.