Ba'Amurka Ta Farko Da Ta Fara Zuwa Kololuwar Tsauni Na Biyu Mafi Tsawo A Duniya

Vanessa O’Brien itace Ba’Amurka ta farko da ta fara zuwa kololuwar tsauni na biyu mafi tsawo a doron kasa. Matashiya Vanessa, ta dau alwashin komi rintsi sai taje inda mafi akasari mazake zuwa, kololuwar tsauni mai hadarin zuwa.

Tsaunin dake tsakanin kasar Pakistan da China, da akema lakani da K2, shine tsauni mafi tsawo, wanda hawanshi yake da matukar wahala ga kowane irin mahaluki. Anyi kiyasin cikin mutane hudu dake hawa tsaunin daya na mutuwa a kan hanyar kaiwa karshen shi a kowace shekara.

Vanessa da ita da sauran abokan tawagarta su 12, sun kwashe tsawon kwanaki dari biyu da casa’in da biyar 295, suna tafiya zuwa kololuwar tsaunin, tafiyar da ta dauke su kimanin tsawon watanni goma 10.

Ita dai mai shekaru 52, tsohuwar ma’aikaciyar bankice, kuma ‘yar jihar New York a kasar Amurka, bayan kaiwar su kololuwar tsaunin, sun dasa tutar kasar Amurka. Hukumomin kasar Pakistan sun karrama ta, da tutar kasar, a ranar 28 ga watan Yuli.

Wannan tsaunin shine tsauni mafi hadari wajen hawa a fadin duniya, kimanin shekaru 39 da suka wuce an samu wata Ba’Amurka ta taba yunkurin zuwa, kololuwar dutsen, tun daga wannan shekarar ba’a sake samun wata mace ba, sai a wannan shekarar.

Wannan shine karo na uku da Vanessa, ta taba gwada zuwa saman tsaunin nan, a shekarar 2015, saboda matsannanciya hunturu bata iya zuwa karshe ba, haka a shekarar 2016 ta kasa zuwa, a sanadiyar munmunan hadarin da matafiya a shekarar suka fuskanta, wanda yayi sanadiyar mutuwar duk mutanen.