Nan Da Shekarar 2040 Za'a Daina Hawa Motoci A Kasar Birtaniya

Masana a kasar Birtaniya sun tabbatar da cewar, hanya daya tilo da za’a magance matsalar dumaman yanayi a duniya itace, a rage yawaitar na’urori dake haddasa zafafar yanayi, musamman akan tituna, wanda suka hada da motoci, mashina, da ire-iren manyan na'urori da manyan kamfanoni ke amfani dasu.

Gwamnatin kasar Birtaniya, na kashe makudan kudade a duk shekara, wajen tsagaita matsalar dumamar yanayi.

Hakan yasa gwamnatin ta fito da wani sabon tsari, da suke sa tsanmanin aiwatarwa a shekaru kadan masu zuwa. Gwamnatin ta cinma matsayar hana hawa motoci akan tituna daga shekarar 2040. Da zummar kawo karshen dumamar yanayi a shekarar 2050.

Kimanin nan da shekaru 23, anasa ran baki daya cikin kasar Birtaniya, babu wata mota ko mashin da zai dinga yawo akan tituna, mutane zasu dinga amfani da, manya-manyan motocin haya, jiragen kasa, da jiragen ruwa don yawo a cikin biranen kasar.

Binciken su ya kara tabbatar da cewar, hayakin da motoci, da mashina ke fitarwa na taimakawa matuka, wajen zafafar dimamar yanayi, da cutar da lafiyar jama’a. Haka wani tsari ne da zai taimaka wajen magance matsaloli da dama, da kuma zummar ganin sauran kasashe a duniya sun dauki wannan sabon tsarin.