Batiri Da Lantarki: Kasar Australia Ta Zama Ta Daya A Duniya

Kamfanin kera motoci na kasar Amurka ‘Tesla’ sun kirkiri wani batiri mai karfin mega 100, sabon batirin shine batiri na farko a fadin duniya da aka taba kirkira mai girma da yakai hakan.

A cewar shugaban kamfanin Mr. Elon Musk, wannan shine karo na farko da aka taba kirkirar batiri da ya kai girman haka, duk wadanda ake kirkira iyakar su karfin mega 40.

A ‘yan kwanakin baya ne kamfanin suka dauki wani alkawalin kirkirar batirin, don agazama yankin kudancin kasar Australia, biyo bayan dauke wuta da akayi a sanadiyar wata guguwa a shekarar da ta gabata.

Dubun dubatar mutane ne suka shiga cikin halin kakanikayi a sanadiyar dauke war wutar. Don haka kamfanin tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar, da wani kamfanin kasar Faransa, suka dauki alkawalin wadatar da yankin da wutar lantarki.

Wannan batirin zai dinga rikewa da adana wuta na tsawon kwanaki da za’a dinga amfani da ita kadan-kadan, batare da daukewar wuta a yankin ba. A cewar mahukunta a kasar ta Australia, wannan babbar nasara ce kwarai, ganin cewar yankin yanzu haka sune wadanda sukafi ko ina karfin da girma wajen ajiyar wutan lantarki a fadin duniya.

Hakan kuma yana nufin cewar wannan tsarin zai basu damar shiga layin farko, a fadin duniya wajen ajiyar wuta ta zamani. Karkashin tsarin sabon tsarin wuta a zamanance ‘Renewable’ yankin zasu daina amfani da tsohon tsarin samar da wutan lantarki.