Ranar Tunawa Da Sojojin Da Suka Kwanta Dama A Amurka
Wata tsohuwar takardar Fosta tun a shekarar 1936 ko 1937, wadda ke nuna wani dan yaro da wani soja suna sara ma juna, yayin da wata karamar yarinya take mikawa sojan furanni. (photo courtesy of the Federal Art Project in New York, 1936 or 1937]
Wasu sojojin Amurka suna neman kaburburan abokansu a bayan da aka gudanar da bukin Ranar Tunawa da 'Yan Mazan Jiya a makabartar Brookwood dake garin Surrey, kudu da birnin London a ranar 30 Mayu, 1945,
Bukukuwan ranar Tunawa da 'Yan MKazan Jiya a garin Ashland, karamar hukumar Aroostook dake Jihar Maine, Mayun shekarar 1943.
Sojojin Amurka da na NATO sun tsaya shiru na wani dan lokaci a lokacin bukin Ranar Tunawa da 'yan Mazan Jiya a sansanin sojan Amurka na Camp Eggers dake Kabul, Afghanistan, ranar 26 Mayu 2008.
Wasu tsoffin sojoji suna saka tutoci a jikin kowane kabari a Makabartar Kasa ta Arlington dake Jihar Virginia, ranar 26 Mayu, 2016.
Tutar Amurka a gefen sunayen da aka rubuta a jikin bakin dutse a hubbaren tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a lokacin yakin Vietnam a Washington, DC. An yi kiyasin cewa sojojin Amurka su dubu 58 ko fiye da haka ne aka kashe a lokacin yakin na Vietnam.
Kwamandan sojojin kasashen waje a Afghanistan, Janar John F. Campbell,(na biyu daga dama) a lokacin bukukuwan karrama sojojin da suka kwanta dama, ranar 25 Mayu 2015 a babbar hedkwatar sojojin Amurka dake Kabul, Afghanistan.