Gwamnatin Amurka, Zata Haramta Amfani Da Kwamfuta A Jiragen Sama

Gwamnatin kasar Amurka, na wani yunkuri na hana matafiyan kasa-da-kasa a jiragen sama, amfani da kwamfutar hannu ‘Laptop’ a yayin tafiya a sararrin samaniya. A cewar shuagaban hukumar tsaron cikin gidan Amurka ‘Homeland Security’ Mr. John Kelly, a yayin zantawa da manema labarai.

Yayi wannan furucin ne a ganawar su da gidan talabijin na ‘Fox News’ inda yake cewar, barin mutane suna shiga cikin jirgin sama, da kwamfutar su wani barazana ne ga tsaron kasar.

Domin ‘yan ta’adda na iya amfani da kwanfuta wajen sace jirgi, da bayanai, ko aikata duk wani aikin ta’addanci. Sai ya kara da cewar, wannan tsarin zai shafi kamfanonin jirage 50, da suke shawagin shige da fice cikin kasar a kowace rana.

Wanda suke sauka a garuruwa 10, na kasar Amurka, mafi akasarin jiragen sukan zo daga kasashen Larabawa da kasashen Arewacin Afrika. Tsarin dai zai bama matafiya, damar saka kwamfutar su a cikin kayan su da ake sakawa a cikin bayan jirgi.

Ana sa tsammanin kimanin jirage 3,250 za suyi kai kawo cikin kasar daga kasashen turai, a wannan tsakanin. Kasar Birtaniya kuwa ta dauki irin wannan matakin, musamman idan jirgi ya taso daga kasashen Turkey, Lebanon, Jordan, Egypt, Tunisia da Saudi Arebiya.