Macce Mai Kamar Maza, Ta Tsallake Rijiya Da Baya A Duniyar Wata

Masana bincike a duniyar wata, sun samu nasarar gyara da garon bawul, ga jirgin kasa-da-kasa dake sararrin samaniya. Kwanaki uku kenan da aka samu ‘yar karamar tangarda a jirgin.

Kwamandan jigrin Peggy Whitson, mace ta farko a duniya da tafi kowa ilimi akan tukin jirgin shiga sararrin samaniya. Ta samu nasarar gyara akwatin da ke dauke da bayanai, a dai-dai lokacin da suke cikin duniyar wata da kimanin tafiyar fiye da kilomita 400 a cikin duniyar wata.

A ranar Asabar da ta gabata ne, hukumar binciken sararrin samaniya ta NASA, tayi wani yunkurin aika mutun, duniyar wata don magance matsalar, amma basu kaiga yin hakan ba, sai ga mace mai kamar maza ta taka muhimmiyar rawa, wajen magance matsalar.

Yunkurin matashiyar Peggy, abun yaba mata ne wajen ganin an shawo kan matsalar, gabanin shigar su wani mawuyacin hali. Hakan na nuni da cewar, ana iya samun karin irin wannan mace a duniya.