Kasar Thailand Ta Ja Baya Da Yunkurin Rufe Shafin FaceBook A Kasar

Sakatare Janar na kafafen yada labaran kasar Thailand Takorn Tantasith

Gwamnatin kasar Thailand, taja baya bisa yunkurin ta na hana amfani da shafin facebook a daukacin kasar. A ranar Talata ne kwamnatin tayi wannan yunkurin, sai dai sun bama kamfanin wasu sharudda da cewar sai kamfanin sun rufe wasu bayanai da take ganin sun sabama ka’idojin su.

Gwamnatin ta bukaci kamfanin na facebook da su kulle wasu labarai da aka saka a shafin, fiye da labarai 130, wadanda suke ganin su a matsayin barazana ga tsaron kasar. Mafi akasarin bayanan sun kaucema dokokin kasar.

Da yawan labaran batanci ne ga sarkin su, wanda idan aka samu mutun da irin wannan laifin, za’a iya kai mutun gidan jarun na tsawon shekaru 15, gwamnatin soji ta dauki zargin masarauta a matsayin babban laifi, tun bayan kwatar mulki da su kayi, kimanin shekaru uku da suka wuce.

A cewar sakatare janaral na kafafen yada labarai ta kasar Thailand Takorn Tantasith, kamfanin na facebook, sun bukaci takardu daga kotu kamin su aiwatar da bukatar gwamnatin, suna sa ran kamfanin zai bi doka. Ya kara da cewar, kamfanin facebook suna bada hadin kai matuka.