Tsohuwar shahararriyar ‘yar wasan kwallon ‘Tennis’ ta duniya Maria Sharapove, idan Allah ya kai rai ranar 16 ga watan Mayu, zata san makomarta ko zata shiga cikin jerin ‘yan wasa da zasu fafata a gasar zakaru na kasar France.
‘Yar wasan mai shekaru 30, ta tafi hutun dole na tsawon watanni 15, biyo bayan samunta da akayi tana amfani da wani magani, dake kara mata kuzari.
A tabakin shugaban kungiyar ‘yan wasan Tennis ta kasar Faransa Mr. Bernard Giudicelli, zai kira ‘yar wasan kamin a dauki wani mataki nagaba.
Zai kuma kokarta ya tattauna da duk wadanda suka kamata, don ganin an sassauta mata hukuncin. ‘Yar wasan dai ta zama zakara a fagen, inda ta lashe kofi sau biyu a jere.
Za’a fara gasar dai idan Allah, ya kai rai ranar 28 ga watan Mayu, a jiya ne aka ruwaito cewar, ‘yar wasan tafara atisaye tun bayan dawowarta daga hutun dole. Yanzu haka ta shirya buga wasa da dan kasar Italy Roberta Vinci.