Shafin Wikipedia ya bayar da ma’anar mentorship a matsayin wata dangantaka tsakanin wani da ya san wani abu ko yake da ilimin taimakawa wanda bashi da shi, domin sa shi a kan hanya.
Shine kuma mutumin da yake ganin baiwa da Allah ya yi wa mutane, wadanda su kansu basu san suna da ita ba, ya kuma taimaka musu da hanyar da zasu ci moriyar baiwar.
Me yasa nake rubutu kan wannan batu na sa wani kan hanya Mentorship?
Kwanannan naji maganar da wani yayi a wani taro kan karancin irin wannan taimako na sanya wani kan hanya, musamman a arewacin Najeriy. Tabbas na yarda da abin da yace, wanda hakan ya sa na fara tunani kan cewa ni kaina me na yi?
Ana haka ne, sai kawai wata ranar jumma’a ina zaune a ofis, sai ga wadansu mutane daga kampanin Washh sun zo wuri na don su bani labarin yadda sana’arsu take bunkasa tare da yin godiya kan irin taimakon da na ba su, na sa su kan hanya.
Abin ya bani mamaki sosai, domin ban taba zaton cewa zan yi tasiri ga kowa ba kamar haka. Ni kawai ina buga-buga ne kawai amma sai ga shi. Yanzu, daga cikinku mutane nawa ne ke kokarin taimakawa wasu domin sa saka su a kan hanya?
Daga cikinmu, mutum nawa ne suka taba taimakawa mai gadin gidansu, wanda ke kokarin kafa ‘yar tireda a gaban gidan da yake aiki. Ka taba tunanin taimaka masa da shawarar yadda zai gudanar da wannan sana’a ta sa da yadda zai yi tattalin kudinsa?
Shin baza ka so a ce watarana wannan ‘yar tiredar ta bunkasa ta zama babban shago irin su Shoprite ba?
Yanzu haka kana da ilimi sosai, ba mamaki ma kana da digiri na biyu, kuma shahararren ‘dan kasuwa amma baka taba taimakawa ko mutum ‘daya ba wajen ‘daura shi a hanya.
Watakila direban nan na gidanka ko kuma mai dafa maka abinci, Allah yayi masa wata baiwa, amma kai kana kallonsa ne kawai a matsayin direba ko mai dafa maka abinci har karshen rayuwarsa.
Hakan yana faruwa ne saboda mugunta irin ta mu, muna duba baiwar da Allah ya bamu mu da ‘ya ‘yan mu ne kawai?
Kasarmu ba zata taba ci gaba ba kamar sauran kasashen duniya, har sai mun fara taimakon junanmu muna ‘daura wasu akan hanya, muna basu dama. Muna barin wasu suna gadarmu kan mukaman siyasa, bawai kawai sai ‘ya ‘yan mu ba.
Saboda haka ina mika godiya ta ga duk mutanen da suka ‘daura ni akan hanya. Na gode. Ga kuma wadanda ke kallo na a matsayin wanda ke taimaka musu, ku nemi wasu kuma ku taimaka musu wajen ‘daura su kan hanya.
Mu ci gaba da aikata wannna aikin na Alkhairi.
Ku tuna cewa, ba wai tsawancin rai ke da tasiri ba illa yawan rayukan da ka taimakawa har suka yi tasiri.