A shirinmu na wasu muhimman mata da suka taka rawa a al’ummarsu, a satin da ya gabata mun alkawarta wa masu sauraro kawo ci gaban hirar da muka yi da wata fittaciyar lauya da ta ga jiya take ganin yau, Fatima Ado Muhammad
Idan ba a manta ba, Malama Fatima ta bayyana mana irin gwagwarmayar da ta fuskata a bangare karatu, kama daga karatunta na farko har zuwa yadda aka yi ta zama lauya.
Ta kara da cewa, akwai daya daga cikin malamin da ke basu darasi mai tsangwama da takurawa dalibai, amma hakan bai kashe masu gwiwa ba, sai ma kara karfafasu da ya yi.
Fatima ta ce matasa a yanzu babu tsoron ubangiji, kama daga yadda suke sanya sutura, zuwa tarbiya ga nagaba da su, da kumma ingancin karatun nasu, lamari sai dai addu'a.
Barista ta ce lokaci yayi da matasa zasu farga , a cewarta a yanzu tun daga tushe matasan ke sanya algus a harkar karatunsu, inda dalibai suka raja’a ga wani abu da suke cewa ‘miracle centers’ inda ake basu satar amsa, a makarantun sakandire.
Daga karshe ta ja hankali matasa da su sake tunani su san cewar karatu shi ne kadai abin sawa a gaba domin cimma bukatun rayuwa.