Babban kalubalen da harkar Hip Hop ke fuskanta a kasar Hausa, bai wuce rashin samun kamfanin da ke dillanci mawaka wajen daukar sauti, tallatasu da ma kasuwancin wakar da suke yi, a cewar shahararren mawaki, marubuci "Billy O".
Bello Ibrahim "Billy O" ya ce kawo yanzu dai, al'ummar kasar Hausa sun karbi wakar Hip-Hop ta Hausa, fiye da yadda aka karbi wakokin soyayya da ma na nanaye. Ya ce abin takaici ne yadda gwamnmati bata maida harkar wakar Hip Hop da muhimmanci, a matsayinta na hanyar samar da kudaden shiga ga kasa, da kara karfafama matasa.
Ya ce a yanzu an kara samun wayewa, kuma ana karbar harkar ta inda duk wani matashin da ya tashi a yanzu, kuma yake harkar waka toh lallai ya fi zabar bangaren Hip-Hop ne.
Ya ce wakar Hip-Hop ta fi yiwa wanda yayi karatun boko adon, a cewarsa wakar na tafiya da boko, domin waka ce da ake yinta ta hanyar yin yanga a salo da yadda ake rereta.
Billy O, a yanzu dai Hip-Hop ta samu karbuwa domin har kananan matasa sun fara karbar ta, don nishadantarwa da ilmantar da sauran matasa.
ku biyo mu domin jin cikakkiyar hirar mu da jigo a harkar Hip-Hop "Billy O" dangane da matsayin wakar Hip-Hop da kuma wasu daga cikin kalubalen da suke fuskanta.
Your browser doesn’t support HTML5