Salisu Ja’afar Dalhatu wanda aka fi sani da ‘Sharu Salisu Gentle’ ya ce yana wakokin da suka shafi zamantakewar Hausawa, a yunkurin fadakar da alu’mma, muhimmanci zaman tare mussaman ma ganin yadda dabi’a Hausawa ta tabarbare.
Ya ce yakan yi wakokin da suka shafi sha’anin aure, abubuwan da ke kawo mutuwar aure, matsalolin mata a bangaren zaman aure, tare da nuna amfani hakuri a zamantakewa.
Sharu Gentle, ya ce malan Bahaushe na da matsalar zumunci a yanzu, dubada yadda a yanzu ba'a zumunci, sai mutun yana da abun hannunsa za’a yi da shi, wakokinsa na nuni da ladan da ke tattare da mai sada zumunci.
Ya kara da cewar, a yanzu bakuwar al’ada na neman kawar da al’adar da iyaye da kakanni suka tashi da ita, ya ce babban burinsa a harkar waka, bai wuce ganin cewar sakonninsa sun isa inda yake so.