Kamfanin Apple Sun Shiga Tseren Samar Da Mota Mai Tuka Kanta

Hamshakin kamfanin wayoyin Apple, zasu shiga cikin babbar gasar samar da motoci masu tuka kansu. Ganin cewar kamfanin na Apple sun taka rawar ganin wajen juya duniyar wayoyi a fadin duniya.

Domin kawo karshe, da nuna kwarewa a komai, kamfanin na Apple sun samu takardar shedar fara amfani da mota mai tuka kanta, wanda hukumar kula da motoci ta jihar California ta basu.

Suna ganin cewar wannan wata damace, da zasu nuna ma duk kamfanoni da suka shiga cikin wannan sana’ar lokaci mai tsaor, cewar basu san komai ba.

Musamman idan aka shiga fannin kimmiya da fasaha. Ya zuwa yanzu dai, zasu fara amfani da motoci uku kirar Lexus RX 2015, mai amfani da haske rana, wanda zasu saka mutane shida a cikin motar.

Yayin lokacin gwaji, doka ta bukaci sai mutane sun shiga cikin motar, wanda idan wani abu ya faru mutane sai su cigaba da tuka motar.

Kamfanin dai sun bayyanar da cewar, sun shigo wannan sana’ar ta motoci ne, don nuna bajinta, duk dai da cewar basu bayyanar da ainin niyar su da shiga sana’ar ba. Amma idan lokaci yayi jama’a zasu gani.