Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Duba Yadda Za A Dage Dokar Amfani Da Wayar Hannu Cikin Jirgi


Gwamnatin Amurka na duba yadda zata dage dokoki da ka’idoji da zasu ba matafiya a jirgin sama damar amfani da wayar hannu.

Shawarar wadda shugaban hukumar sadarwa Tom Wheeler, ya gabatar a shekarar 2013, zata duba tsohuwar dokar nan data hana amfani da wayar hannu a cikin girgin sama bisa la’akari da network din wayar hannu ka iya yiwa layin sadarwar matukin jirgin katsalanda.

Wheeler, ya bayyana cewa sakamakon sababbin hanyoyin sadarwar zamani na jiragen sama da aka samu, ana iya takaitawa ko dakatar da wannan doka.

Duk da haka, a karkashin wannan sabuwar dokar, zata bukaci matafiyi ya kashe wayarsa ta hannu a yain da tashi da saukar jirgin saman, amma fasinjoji zasu iya kunna wayoyinsu a yayin da jirgin ke sararin sama.

Wannan shawara ta samo asali ne daga ofishin shugaban sadarwar wanda ya barwa shugaban na yanzu Wheeler, kujera Mr Ajit Pai, wanda ya bayyana cewa bai yi imanin dokar na da wani tasiri ga jama’a ba.

Wannan shawara ta ba matafiya damar amfani da wayoyinsu na hannu dai ta sami martani daban daban mabanbanta daga kungiyar matuka jirgin sama, da ma’aikatan jirgi, inda wasu ke ganin cewa hakan zai hana matafiya da dama sakewa su huta yayin da ake tafiya domin wasu zasu yita Magana ta waya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:19 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG