Tsohon dan wasan kasa-da-kasa Nduka Ugbade, ya bayyanar da kwarin gwiwar shi akan ‘yan wasan Super Eagle. A wasan da zasu gwabza da kasashe biyu. ‘Yan wasan zasu buga wasan kawance da kasashen Senegal da Burkina Faso.
Mr. Ugbade, ya bayyanar da hakan a wata zantawar da yayi da manema labarai, ‘yan wasan Najeriya dai zasu hadu da ‘yan wasan kasar Senegal a filin wasan Barnet idan Allah ya kaimu gobe.
Za kuma su hadu da ‘yan wasan kasar Burkina Faso a filin wasan Etalons, nan da kwanaki hudu. Wannan wasan kawance da za’a buga a kasar Ingila, zai ba ‘yan wasan damar shiryawa ne don tunkarar wasan cin kofin kasashen Afrika a shekarar 2019.
Ana dai sa ran fara wannan wasan a watan Janairu idan Allah ya kai rai. Haka za a buga wasan cin kofin duniya na FIFA 2018, wanda za a buga a watan Agusta duk a cikin shekara mai zuwa.
Shi dai Ugbade, shine dan Afrika na farko da ya taba lashe kofin duniya, na ‘yan wasa kasa da shekaru 17 a shekarar 1985 inda lokacin klob din su ya hada da matasa kana da kwararru a harkar kwallo. Ya kara da cewar yana murna da irin kokarinsu na zama zakaru a kasashen Afrika.