Gwamnan jihar Osun Rauf Aregbesola, na daya daga cikin masu sha’awar Tamola, kana kuma masoyi ga kungiyar kwallon kafar Arsenal. Yayi kira da babbar murya ga shugaban kungiyar Arsene Wenger, da ya gaggauta murabus akan matsayin shi na shugaban klob din.
Wannan kiran ya biyo bayan wasan da aka gwabza tsakanin ‘yan wasan na Arsenal da ‘yan wasan kungiyar Liverpool, inda aka tashi da ci uku da daya 3-1. A wasan zakaru na firimiya lig jiya lahadi.
Gwamnan dai mai shekaru 59, ya fada a baya cewar kocin kungiyar Arsenal dan asalin kasar Faransa, yana gabda komawa gida, domin kuwa ya kwashe shekaru kusan ashirin yana aikin kwallo, don haka lokaci yayi da ya kamata ya huta.
Kocin Arsen Wenger, ya rubuta a shafin kungiyar na twitter cewar “Ina kara godiya ga kungiyar Arsenal da karamci” inda dan majalisar wakilai Ayo Omidiran, ya maida mishi da martani da cewar “Oga Wenger ba zai tafi ko ina ba”
Wani masoyin shugaban klob din Wenger, Omidiran ya rubuta a shafin shi na twitter da cewar “kungiyar Arsenal sai mutuwa”, inda shi kuwa gwamnan jihar Osun Aregbesola, ya bashi amsa da cewar “Amma kwakwalwa ta na cewar kayi kuskure” Domin kuwa kungiyar Arsenal na da masoya da yawa a kasar da tafi kowace kasa yawa a nahiyar Afrika.