Ahmad CAF: Amaju Na Daya Daga Cikin Wadanda Suka Bani Kwarin Gwiwa!

Shugaban NFF Amaju Pinnick

Shugaban kungiyar kwallon kafar FA, na kasar Madagaska, Ahmad Ahmad, ya bayyanar da Amaju Pinnick, shugaban kwallon kafar kasar Najeriya, a matsayin wanda ya fara bashi gwarin gwiwar shiga gasar neman shugabancin kujerar kungiyar kwallon kafar kasashen Afrika, CAF.

Ahmad din dai ya bayyanar da hakan a yayi wata ziyara da ya kai kasar Najeriya, don neman goyon bayan, ‘yan kungiyar, don tunkarar zaben da za’a gabatar a ranar goma sha shiga, ga wannan watan.

Inda yake kokarin karawa da shugaban kungiyar mai ci, Issa Hayatou, Ya bayyana ma maneman labarai cewar “Lallai dole abubuwa su canza a cikin tsare-tsare na kungiyar kwallon kafar”

Ya kara da cewar akwai bukatar sauyi na yadda muke gudanar da ayyukan kungiyar, da suka shafi horas da koci-koci, rafalis. Akwai bukatar samar da horas wa ta musamman ga kocis na tsawon kwanaki goma zuwa sha biyar 10-15.

Hakan zai sa a samu nagartattun koci, da kuma sama musu aiki cikin gaggawa. Sai yace, tabbas ba buri na bane na zama shugaban kungira CAF, amma abokan aiki, su suka bani wannan kwarin gwiwar, musamman Amaju Pinnick, yana daya daga cikin su.

Jim kadan bayan kammala taron kungiyar kwallon kafar duniya FIFA, da aka gudanar a kasar Mexico, a shekarar da ta gabata. Ya kirani ya bayyana mun cewar, lallai akwai bukatar canji a cikin kungiyar nan tamu.