Motar Chevrolet-Bolt Ta Wuce Tsara, Ta Zama Motar Shekarar 2017!

Motar Shekarar Bana 2017

Shahararren kamfanin motocin kasar Amurka, “General Motors” masu motoci kirar “Chevrolet, Chrysler, Silverado” sun karbe kambun tsarin motoci masu amfani da wuta a duniya. Kudin motar na farawa daga $37,495, kimanin naira milliyan goma sha daya.

A yau litinin ne dai aka bama wannan kamfanin, lambar yabon. Motar da ta jawoma kamfanin wannan nasarar itace “Chevrolet Bolt” ita dai motar wadda fitattcen mai zanen motocin kamfanin, dan Najeriya ya zana Jelani Aliyu.

An dai ayyanar da kamfanin a matsayin kamfanin, da ya zama zakaran gwajin dafi, a yankin Arewacin kasar Amurka. Kamfanin ya doke kamfanoni biyu, wanda suka hada da kamfanin Volvo S90, da Genesis G90. A dai-dai lokacin da aka gudanar da bukin, wanda masana suka bayyanar da tsarin wannan kamfanin ya wuce na saura.

Motar “Chevrolet Bolt” itace motar da ta mamaye kasuwar motoci, ganin cewar motar tana da tsarin amfani da mai tare da hasken rana. Jelani Aliyu, yana daya daga cikin matasa masu basira, da suka farfado da kasuwar kamfanin General Motors, wanda a shekarun baya kamfanin ya nemi durkushewa.

Ana iya alakanta tasowar kamfanin da irin basirar da Allah, ya bama Jelani, don amfani da basirar shi wajen zanen motoci da su kayi kasuwa, ba kawai a kasar Amurka ba, harma da kasuwannin duiniyar motoci.