Tsibirai Masu Ban Sha'awa, Kada A Ba Mutun Labari, A Shekarar 2017!

Tsibirai Masu Kyau A Duniya

Lokaci yayi da masu sha’awar tafiye-tafiye zasu fara hada akwatunan su, tafiya don yawon bude ido a kowace nahiya cikin shekarar 2017, ta matso. Sakamakon rahoton wani kamfani mai zaman kanshi “American Express Global Business Tracel” sun bayyanar da cewar, a wannan shekara ta 2017, kudin jiragen sama zasu sauka matuka.

Wasu zababbun wurare Ina-da-ina ya kamata mutun ya ziyarta a wannan shekara, masana suna ganin cewar wasu garuruwa a wasu kasashe suna da muhimanci idan mutun ya ziyar ce su, a wannan shekarar. Na farko shine Tsibirin Mazatlan, na kasar Mexico, tsibiri ne mai taken tsimi da tanadi, kuma ga ban sha’awa da kayatarwa.

Dajin kasar Afrika ta kudu, na daya daga cikin wurare da mutane zasu ziyarta don shakatawa, da bude ido. Garin San Juan, na kasar Puerto Rico, dake yankin kudancin kasar Amurka, na daya daga cikin garuruwa masu dunbin tarihi da sha’awa. Kasar Chile, a yankin kasashen turai, tana iya zama cikin wurare masu ban sha’awa haka rayuwa a yanki ba tsada.

Garin Crete, dake yankin kasashen turai, yana da ban sha’awa, kana yanzu haka yadda darajar kudaden wasu kasashe suka fadi, yasa yawo zaiyi dadi idan mutun yana da ‘yan kudaden shi. Haka kasar Morocco, kasace mai dinbin tarihi, da al’adu iri daban-daban, kana suna da abinci kala-kala, da kasashen duniya ke sha’awa.